Rikicin 'yan Shi'a: Sojoji sun kafa hujja da Trump kan harbin 'yan Shi'a
Rundunar sojin Najeriya ta kafa hujja kan bude wa 'yan Shi'a wuta da wani faifan bidiyon na Shugaban Amurka Donald Trump, wanda a ciki shugaban yake cewa sojoji za su iya amfani da karfi kan baki 'yan ci rani da ke jifansu da duwatsu.
"Idan suka yi jifa da duwatsu... ku dauka sun yi da bindiga ne," in ji Mista Trump a wani faifan bidiyo.
Jami'an tsaron Najeriya sun kama mabiya Shi'a 400 bayan wani mummunan artabu na tsawon kwanaki a Abuja
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki sojojin kasar da kashe 'yan Shi'a, inda kuma ta ce zanga-zangar 'yan Shi'ar ta lumana ce.
Sai dai mai magana da yawun sojojin kasar Burgediya Janar John Agim ya ce sun yi amfani da harsasai masu rai ne ga masu zanga-zanga saboda suna dauke da makamai.
Ya ce: "Wannan ne abin da Mista Trump yake magana a kai."
Shafin Twitter na rundunar sojin kasar ya wallafa bidiyon Shugaba Trump da rubutu kamar haka: "kalli wannan bidiyon, ka yanke hukunci".
No comments