Littafin mai sona fita ta 33

Littafin mai sona fita ta 33


Sun shigo falon tare da sallama, imran ya fito zai wuce masallaci kenan ya daga kansa suka hada ido da Ruhaimat yayi saurin dauke kai yace "mami barka da xuwa Ku karasa suna ciki" yayi wucewarsa Ruhaimat de tana mamakin sauyin da yayi bahaka ta sanshi bah..Momi tayi farin ckn ganinsu a nan sukayi magrib sannan suka koma falo suna hira yasmeen ta shigo tare da sallama tana cewa "wash..Momi na gaji wllhi nayi rawa Yau ba kadan bah" tsaki Momi ta ja tare da cewa " Allah ya shirya.. Ki jira mijin naki don ya shigo yana tambayar ki, dama karya kika min da kika ce shiya baki izinin xuwa gidan bikin" dariya tayi sai ynxu ta kula da su mami tace "lah..Momi baki mukayi" "Mara kunya..wannan mahaifiyar sadeeq ce tare da matarsa" murmushi tayi "ina yinin Ku" mami ta amsa ckn sakin fuska , Ruhaimat ta juya kenan suka hada ido yasmeen ta bude baki cke da mamaki tace "ahh..wannan ce matar sadeeq?, amma ai ba ita bace wacce na Sani" "amaryar sa kenan sunanta Ruhaimat" tabbas yasmeen tasha ganin hotunan Ruhaimat ckn wayar imran kuma ta San cewa imran yana matukar kaunar Ruhaimat.. Amma mamakinta shine yanda ta canza ta kara kyau ga kuma dressing nata mai daukar hnkli ..sabanin da ta Santa da hijabi tana mata kallon bagidajiya, da wannan tunanin ta wuce dakin Momi "hajiya mami kina ganinta ai..haka nake fama kullum gani nan sai raba fada, wllhi nagaji abun nasu baya karewa" mami tace "meya kawota nan gidan bayan ga gidan mijinta" "wllhi bata da hankali ko kadan iyayenta sun sangartata..ni tausayin imran nake ji hakuri kawai yake ya xuba mata ido" "gskiya kiyi kokari ki wayar mata da kai don na lura tNa ckn duhu batasan ya ake rayuwar aure bah..kina cutar da danki a banxa ga mata nan birjik meyasa kuka xaba masa wannan fisararriyar" "uhmm kedai bari kawai..xanyi bakin kokarina" "Allah yasa mu dace" wayar Ruhaimat ya sake vibrating a karo na 5 murmushi mami tayi tace " chewing gum naki koh..nasan yana can yana jira tashi mu tafi" Momi tayi jugum tana kallon Ruhaimat.. Allah sarki imran da Ibrahim sunyi rashin mace ta gari .."toh Momi imran mun tafi" "nagode kawata Allah ya bar xumunci..dota nagode koh" daki ta wuce ta fito dauke da wata bakar Leda ta mikawa Ruhaimat dakyar ta karba tare da yin godiya daga nan suka wuce gida.


  Sati  1 su mami sukayi daga nan suka koma Abuja tare da Mimi Ruhaimat tayi kewar yarinyar sosai don ita take kipin nata busy...wata sabuwar rayuwar soyayya suka shimfida tamkar xasu hadiye juna tare suke yin komai idan yana office ma suna makale da juna a waya haka Rayuwa ta cigaba suna rokon Allah akan samun haihuwa don har ynxu shiru kake ji kamar an shuka dusa.xaune yake bisa carpet grass a yayinda Ruhaimat tayi matashi da cinyarsa a garden din gidan suke suna shan iska tana karanta masa littafin *kissoshin annabawa* yana jin dadin tarihin annabi Yusuf da take karanta masa sai faman lumshe ido yake, Momi ce tare da yasmeen suka shigo masu gadi suka shaida musu inda masu gidan suke kai tsaye wajen garden suka nufa yasmeen na raba ido tana mamakin girma da kyawun gidan saboda bata taba xuwa bah gidan da sadee ta xauna ne taje sau  1.sadeeq ne ya hangosu yace "maini munyi baki tashi ki xauna" ckn sauri ta tashi ta sanya hijabinta don kananan kayane a jikinta "lah..Momi Yau kece a gidan namu..barka da xuwa" ckn tsananin kunya Ruhaimat ta musu maraba , sadeeq yace "mu je ciki koh" daga nan suka koma ckn gida a falo suka xauna Ruhaimat ta jera musu kayan motsa baki bayan sun gaisa sadeeq ya tashi ya fita Ruhaimat tabi bayansa a bakin motarsa ya tsaya nan suka rungumi juna ya manna mata peck a kumatu yace"ki kula kanki idan sun tafi ki kirani ok.." "Ok..u too takkia" "Lov u" "Lov u more..banda kallon mata" murmushi yayi tare da cewa "ni me xan kalla a jikin wata mace..I have u I have everything" murmushin jin dadi take daga nan ta daga masa hannu yaja motarsa ya tafi.duk abunda sukayi akan idon yasmeen mamaki ne karara a fuskarta..dama haka  Ruhaimat ta iya soyayya? Yaushe ta waye haka? Xama tayi bisa kujera tana bin falon da ido har taji ta raina kanta..ikon Allah kenan wai Ruhaimat ce ckn wannan katafaren gida haka?, koda Ruhaimat ta shigo yasmeen bata daina kallonta bah..minti 50 sukayi a gidan sannan suka mata sallama.. Cake doughnut da kunun Aya ta xuba musu ckn bakar Leda sai kayan makeup da turarukan humra masu kamshi ta rakasu har bakin mota ta ajiye ledojin a gidan baya godiya sukayi yasmeen ta ja motar sika koma gida. Momi ta kula da halin da take ciki tun bayan dawowarsu daga gidan  Ruhaimat "yasmeen meke damunki na ga kin xama wani iri" "Momi magana zamuyi" "ok go ahead"......by hausadaily.com.ng

No comments

Powered by Blogger.