Kun san matar da za ta zama mataimakiyar El-Rufai?

Kun san matar da za ta zama mataimakiyar El-Rufai?



A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamna El-Rufai ya ce ya zabi Dr. Hadiza Balarabe ne domin karfafa gwiwar mata.
Dr. Hadiza Balarabe ita ce babbar sakatariya a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kaduna.
A cewar El-Rufai, manyan ayyukan Dr. Hadiza Balarabe sun hada da kaddamar da shirye-shiryen da suka inganta tsarin kiwon lafiya na jihar ta Kaduna.
Dr. Hadiza ta soma aiki a fannin lafiya na babban birnin tarayya, Abuja a 2004 inda ta kai matsayin daraktar kula da lafiya.

No comments

Powered by Blogger.