An yi jana'izar Janar Idris Alkali mai ritaya a Abuja, babban birnin Najeriya ranar Asabar da rana

Mutane da dama ne - ciki har da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Yusuf Buratai - suka halarci jana'izar Janar din, wanda aka kashe a jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar kasar a watan Satumba.
A ranar Laraba ne rundunar sojojin Najeriya ta gano gawar Janar din a wata rijiya da ke Gushwet a gundumar Shen ta karamar hukumar Jos South a jihar Filato.
Kwamandan runduna ta uku ta dakarun kasar, Birgediya Janar Umar Mohammed ya ce daya daga cikin wadanda suka mika kansu ga 'yan sanda ne ya nuna wa sojoji rijiyar, wadda "ba a amfani da ita."

No comments

Powered by Blogger.